Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Alaa Shaham, mai shekara kimanin ashirin ya mutu ne sakamakon harbin bindiga a kai na sojojin Isra’ila a yankin Qalandia dake tsakanin birnin Qudus da Ramallah.
Shi kuwa Nader Haitham Rayan, mai shekara 16, ya mutu ne sakamakon harbinsa da da sojojin na Isra’ila sulayi masa da harsashai masu yawa a kirji da kuma kai, a sansanin ‘yan gudun hijira na Balata kusa da Naplouse, kamar yadda ma’aikatar kiwon lafiyar ta falasdinu ta sanar, saidai ba tare da yin bayyani ba kan sanadin faruwar lamarin.
Sau tarin yawa dai akan samu arangama tsakanin falasdinuwa Da kuma jami’an tsaron Isra’ila dake kai samame a yankunan Falasdinun da suka mamaye tun cikin 1967.
342/